WATA SABUWA: Ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa (CAN), tayi kira ga DSS dasu binciki Pantami

Shugaban CAN ta ƙasa, Reverend Samson Ayokunle, yayi kira ga hukumomin da abinda ya dace dasu binciki zargin da ake yiwa ministan sadarwa na ƙasa Dr. Isa Ali Pantami.

Idan dai za’a iya tunawa, Pantami ya tada ƙura a ƴan kwanakin nan sakamakon maganganu da yayi tun shekaru aru-aru bisa abubuwan da Al-Qaeda sukeyi a wancan lokacin, wanda hakan yasa wasu mutanen ke kira daya ajiye aikinsa.

Duk da cewar ministan ya amsa faɗin wadannan kalamai da ake zargin sa dasu, amma yayi zargin yarinta da kuma rashin sani akan al’amurra a wancan lokacin.

Amma duk da haka, da yake magana a wani taro da aka gudanar Lagos-Ibadan Expressway, Reverend Ayokunle ya kira hukumomin tsaro dasuyi ta maza su gayyaci malamin.

Ravaren din ya ƙara da cewa: “Me shugabannin hukumar tsaro suke yi ne? Me yan sanda suke yi ne? Me shugaban hukumar tsaro ta farin kaya takeyi itama? Wannan zargin da akeyi bai kamata a ɗauke shi da sanyi sanyi ba. Yakamata a ɗauke shi da gaske. Tunda muna da cikakken bayani, wanda yake a rubuce, wanda yake tabbatar da bayanin nan, wai me yasa sukayi shiru ne? Tambayar nan kada wanda ya tambaye Ni, Ni ba jami’in tsaro bane, bani da amsar ta. Duk wata tambayar da kuke so kuyi, ku tambayi hukumar tsaro ta farin kaya akan me yasa basuyi bincike akan zargin nan ba? Ko akwai dalili? Da zarar sunzo da dalili wanda yake kan tsari kuma amsashshe , shikenan an warware matsalar”. Inji shugaban CAN.

Daga karshe kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya data katse shigowa da makamai da ake mallaka ba bisa tsari ba a cikin faɗin ƙasar, sannan ta bincika tushen da ake samo su.

Yayi kira kuma gwamnati ta dauki ƙarin jami’an tsaro domin warware matsalar tsaro data ƙi ci, ta ƙi cinyewa, inda ya ɗaura laifin a ƙarancin jami’an tsaron idan akayi la’akari da yawan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *