Addini

Wata Sabuwa: Mu Gobe Zamu Ajiye Azumin Mu — Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Spread the love

Sababbin bayanai da suke fitowa gamida da ƙarasowa teburin yaɗa labarai na Mikiya na nuni da cewa, ta tabbata Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ɓara akan batun ajiye Azumin bana.

Bayanan na nuna cewa, biyo bayan binciken ƙwaƙwaf da sukayi na ganin wata da akayi a Jihar Nasarawa, Kurgwi ta Plateau, babban birnin tarayya na Abuja, yasa yake umartar mabiya bayansa dasu ajiye azumi gobe, kuma suyi sallah Litinin.

To sai dai kuma akan batun sallar idi, an ruwaito cewa, Shaihin malamin yace tunda idi nafila ce, ya roke masu binsa dasu bari sai ayita a ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan ƙasa mai tsarki wato Saudiyya, sun zayyana cewa Asabar ɗin nan da muke ciki ta tabbata ba’a ga watan Shawwal ba, wanda hakan ke nuni ga musulmai cewar, azumi talatin za’a yi.

Bugu da ƙari, batun na Sheikh Dahiru Usman Bauchi na zuwa ne lokacin da Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce sai ranar Litinin, biyu ga watan Afrilun 2022 sallah zata kama.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button