Addini

’Yan bindiga sun yi ta kai farmaki ne saboda Musulmai sun kauce daga koyarwar Annabi Muhammadu (s.a.w) – Gwamna Matawalle

Spread the love

“Musulunci shine zaman lafiya. Ba za mu iya aiki da shi ba tare da zaman lafiya ba. Don haka ina kira ga kowa da kowa da su sanya ruhin zaman lafiya da juna domin mu samu albarkar Allah.”

Gwamna Bello Matawalle ya jaddada kudirin gwamnati na maido da zaman lafiya a Zamfara, inda ya koka kan yadda Musulmi suka kauce daga koyarwar Annabi Muhammad (s.a.w), inda yace yana kara tayar da fitina a Arewa.

“Musulunci shine zaman lafiya. Ba za mu iya aiki da shi ba tare da zaman lafiya ba. Don haka ina kira ga kowa da kowa da mu yi ruhin zaman lafiya da kwanciyar hankali domin mu samu albarkar Allah. Mun samu fiye da kaso mai tsoka na tashe-tashen hankula da kuma ayyukan muggan laifuka wadanda ke kawo cikas ga zaman lafiya a jiharmu,” in ji Mista Matawalle. “Saboda da yawa daga cikinmu sun zabi kauce wa koyarwar Annabinmu masoyinmu.”

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Zailani Bappa ya fitar ranar Litinin a Gusau.

“Yau ce ranar da gwamnatin Najeriya ta kebe domin gudanar da Mauludin na bana, maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW),” inji gwamnan. “Ina taya miliyoyin al’ummar Musulmi a jihar da kuma wajen juhar bikin murnar wannan lokaci mai albarka.”

Ya kara da cewa, “Hakika sama da karni 14 da suka gabata, Allah ya yi wa wannan duniya wata ni’ima wacce ke nuna babbar rahamarSa ga bil’adama ta hanyar aiko da manzonsa na karshe don shiryar da mu zuwa ga tsira da hanya ta gaskiya. Bikin namu wata alama ce ta godiya ga Ubangiji da wannan ni’ima ta musamman da ya yi mana.”

Gwamnan Zamfara ya yi wa Musulmi gargaɗi a kan bin koyarwar Annabi gwargwadon ikonsu don su sami albarka a nan da kuma lahira.”

Gwamnan ya umurci malamai a Zamfara da su yi wa’azin zaman lafiya a tsakanin Musulmi tun daga tushe don magance matsalar ‘yan fashi da sauran laifuka.

Ya danganta shigar matasa da aikata laifukan fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran laifuka a Zamfara da jahilcin rayuwa, da kuma kaucewa koyi da Annabi. Wannan, in ji shi, “ya ba da gudummawa ga yawaitar halaye marasa kyau kamar yadda muke gani a cikin munanan dabi’u” kamar su ‘yan fashi, sata da kuma shan muggan kwayoyi.

“Saboda haka, yayin da muke murnar wannan rana ta musamman, ina umartar kawunanmu da kada mu manta da ainihin bukin domin dukkanmu mu yi waiwaye a baya, mu canza salon rayuwarmu da kyau,” in ji Mista Matawalle. “Ina yiwa kowa fatan alkhairi.”

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button