Addini

‘Yar kasar Indiya mai siffar muminai wajen kare muradan addini.

Spread the loveWannar ita ce Ghazala Ahmad, ‘yar kasar India dalibar da take karatun aikin Jarida.

Wannar jakadiyar Allah ce, Jakadiyar Annabi (S.A.W) ce, Jakadiyar addini ce. Tana daga cikin na gaba-gaba a cikin daliban da suka jajirce sai an bar musulmai mata sun saka Hijabi a makaranta

A dalilin hana hijabin ne yasa Indiyawa musulmai mata suka gudanar da zanga-zangar lumana a jiya Laraba, sannan sun nunawa duniya cewa Hijabin nan umurni ne na addinin su na musulunci.

Yanzu haka batun yana kotu a kasar ta Indiya, Malama Ghazala Ahmad ta sha Yabo da addu’a da jinjina a duniyar musulmai, musamman a kafofin sadarwar zamani da ake saka bidiyon nata a Status Saboda yadda take daga murya tana kabbara (ALLAHU AKBAR) a makarantar tasu cikin rashin tsoro, ga kuma ihu na nuna kiyayya da Indiyawa dalibai maza suke mata.

Ya ALLAH ka yiwa iyayen wannar baiwar ALLAH, da kuma iyayenta sakayya da gidan Aljanna, damu kan mu dama namu iyayen, ka dora mu akan jajircewa akan lamuran addinin daka halicce mu domin shi, ako ina muka tsinci kan mu a duniya ka bamu ikon zamowa jakadun addini ba tare da tsoro ko shakku ba, ka karkatar da zukatan mu wajen addini da kare addini, da mutuwa akan addini.

ALLAHU AKBAR !

Daga Bappah Haruna Bajoga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button