Tsaro

Aiki Sai Da Kayan Aiki: Gwamna Zullum ya siyawa Mafarautan Hawul Bindigogi da sabbin motoci domin su kare kansu daga ta’addancin ‘yan Boko Haram.

Spread the love

Gwamnatin Borno ta amince da amfani da bindigogi daga mafarautan yankin kan mayakan Boko Haram.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Laraba, 30 ga watan Disamba, ya wadata mafarautan yankin da bindigogi a karamar hukumar Hawul ta jihar domin tunkarar mayakan Boko Haram.

Gwamnan, wanda mataimakinsa, Umar Kadafur ya wakilta, ya ba da motocin Toyota Hilux guda takwas da sauran kayan aikin da aka nema ga mafarautan yankin da kungiyar ’yan banga a hedkwatar karamar Hukumar, Azare.

Zulum ya ce: “Gwamnatin jihar Borno ba za ta yi kasa a gwiwa ba ko kuma kau da kai daga nauyin da tsarin mulki ya dora mata na kare rayuka da dukiyoyin jama’a kuma za ta ci gaba da mai da hankali wajen tabbatar da cewa cikakken zaman lafiya ya dawo jihar.”

Zulum ya kuma yi kira ga mutanen yankin da su ba da hadin kai ga juna tare da taimakawa jami’an tsaro da bayanai masu amfani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button