Labarai

Aiki Sai Mai Shi: Gwamnatin Jahar Borno Ta Dauki Matasa 2862 Aiki.

Spread the love

Gwamnatin Jahar Borno ta dauki Matasa 2862 Aikin Shara…

A kokarin yaki da talauci Na Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya Dauki matasa 2,862 aikin Shara da Gyara magudanan Ruwa a Maiduguri da kewaye.

Kwamishinan Ma’aikatan yaki da Talauci Na Jahar Nuhu Clark ne ya Shaidawa Manema labarai hakan Jiya Laraba a Maiduguri Fadar gwamnatin Jahar.

Clark yace ma’aikatan Sharan da Ma’aikatarsa ta Dauka Ana biyansu dubu 30 ko wanne wata, Kuma zasuyi Aiki Har wata 6 Sannan Gwamnati zata Basu Jari kowa ya Kama Sana’a.

Har Ila yau Clark yace Ma’aikatarsa ta Bada rancen Kudi dubu 30 Ga Mutane dubu 2500 masu sana’ar Treder A Tashar mairi zasu biya dubu 15 ne kachal cikin shekaru 5.

Sannan Ta bada Rancen Kudi daga Dubu 60 zuwa dubu 500 ga yan kasuwar Waya Na Bulunkutu Wanda Ibtila’in gobara ta shafa duk a cikin Maiduguri.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button