Rahotanni

Ajali: Fasinjoji 3 ne suka mutu sakamakon gobara da wata motar bas ta kasuwanci tayi a Kano

Spread the love

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce fasinjoji mata uku ne suka mutu yayin da wasu 13 suka samu raunuka sakamakon gobara da wata motar bas ta kasuwanci a ranar Talata.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce fasinjoji mata uku ne suka mutu yayin da wasu 13 suka samu raunuka sakamakon gobara da wata motar bas ta kasuwanci a ranar Talata.

Kakakin hukumar kashe gobara Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Motar kasuwanci kirar Toyota Hiace mai lamba XE 222 TRN ta kama wuta a kusa da kwalejin fasaha ta gwamnati da ke karamar hukumar Nassarawa.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne yayin da motar bas da ta tashi daga karamar hukumar Ajingi zuwa Kofar Wambai ta kama wuta.

Sanarwar ta ce jami’an kashe gobara da jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ne suka kashe gobarar tare da ceto mafi yawan wadanda suka jikkata, amma wasu mata uku sun kone kurmus.

Wadanda suka rasu sun hada da Surayya Umar da Zeenai Babaji. Ba a bayar da sunan mutum na uku ba.

Sauran 13 da suka jikkata an kai su Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Direban bas din mai suna Muhammed Gali mai shekaru 35 da Kwandastan motar sa Hassan Danladi mai shekaru 30 ba su samu rauni ba. An mika su ga ‘yan sanda.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button