Tsaro

Akwai Alaka Tsakanin Ta’ammali Da Miyagun Kayan Shaye-shaye Da Matsalar Tsaron Da Ta Addabi Arewacin Nijeriya.

Spread the love

Daga Kais Dauda Sallau

Ba shakka matsalar tsaro abu ne wanda ya addabi arewaci Nijeriya wanda ya haɗa matsalar yan Ƙungiyan Boko Haram, Yan bindiga dadi, faɗan kabilanci, masu satar mutane da sauran su. Hakan ya kara kawo ci baya sosai da talauci ga al’ummar arewa dama Nigeriya gaba ki daya.

Matsayar tsoro a arewacin Nigeriya ya ki ci ya ki cinyewa dudda maƙuden kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a farnin tsoron.

Kuma akasarin masu aikata wadannan miyagun ayyukan matasa ne wanda mafi yawan su ba a cikin hayyacinsu su ke aikatawa wannan miyagun ayyukan ba. Idan mu ka lura dayawa daga cikin masu aikata wadannan ayyukan duk lokacin da a ka kama su sai an same su da miyagun kayan shaye-shaye masu fitar da mutum a cikin hankalinsa irin su ƙwaya da sauran su. Haka ko daga maganganun bakin su idan a ka kama su, za ka fahimci cewa akwai abinda su ke sha mai juya musu tunani, ya kuma cire musu tausayi.

Ya kamata gwamnati su dauki matakai masu tsanani kan masu shiga da kayan maye da masu sayar da shi a ƙasar nan. Matukar gwamnati ba ta tsaya ta yi yaki da harka da kayan maye a ƙasar nan ba, gaskiya akwai matsala, domin za a dinga samu tseko gurin yaƙi da matsalar tsaro da a ke yi a arewacin Nigeriya matuƙan matasan na samun kayan mayen suna sha.

Allah ya ba mu zaman lafiya a kasar mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button