Rahotanni

Akwai Ban Tsoro Akan Kaburburan Da Aka Tono A Libya.

Spread the love

Majalisar dinkin duniya ta bayyana shakkunta akan kaburbura takwas da dakarun Gwamnatin kasar Libya suka tono.

Wannan yankin dai dakarun Gwamnatin Libya sun kwatoshi ne daga hannun dakarun mayakan Janar Khalifa Haftar.

Kwamitin Samarda lafiya na majalisar dinkin duniya ya bayyana hakan a shafin su na Twitter.

Mafi yawan kaburburan takwas da aka tono daga Garin Tarhuna ne.

Dokar kasa da kasa dai ta bada dama ga hukumomi da suyi bincike akan dukkanin kisar gillar da aka aikata domin daukar matakan da suka dace.

Jaridar Daily Sabah ta bayyana cewa yankunan da aka tono wadannan kaburbura sune Tarhana, dakuma yankin kudu maso gabashin Babbar birnin kasar Wato Tripoli.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button