Labarai
Akwai Ban tsoro matuka Ko a film aka kashe 43 ~boss Mustapha ga Pantami.
Wani matashi a shafins sada zumuntar na Twitter Mai suna Boss Mustapha Ya Kai koke ga Pantami A Sashin Sharshi inda matashin Yace Ya Sheikh @DrIsaPantami – muna kawo kukan mu gareka. Dan Allah dan Annabi ka samu ka yi ma shugaban kasa magana. Mutum arba’in da hudu (43) ko wani fim aka kashe lokaci daya abun da ban tsoro.
Dan Allah a taimaka a yi wani abun a kai abun ya fara yawa
Sai shehun malamin ya bashi amsa da cewa..
Mun sha yin hakan, kuma za mu ci gaba da yi in sha Allah. Zan kuma ba shi labarin wannan, kamar yadda na yi magana da Gwamna Zulum jim kaɗan. Allah Madaukakin Sarki Ya tausaya musu Ya kawo karshen bala’in.