Akwai Damuwa Da Bacin Rai Kan Yadda Ake Zubar Da Jini a Arewa, Inji ACSC
Majalisar Tuntuɓa Da Haɗaka Na Arewa na miƙa saƙon Ta’aziyyar ta da Jajantawa ga Gwamnatin Jihar Zamfara da Maigirma Sarkin Ƙauran Namoda, Wasu da ake zargin Ƴan bindiga ne sun kai wa tawagar Sarkin Ƙauran Namoda, Alhaji Sanusi Muhammad Asha hari inda suka kashe ƴan sanda uku da wasu fadawa da ƙanin sarkin.
Majalisar tayi kira da Hukumomi dasu canza salon yaƙi da Ta’addanci a Nijeriya, akwai takaici Ace kullum sai an kashe mutane a Arewa kuma haryanzu matakan da ake ɗauka basu sauya salo ba.
Majalisar kuma tayabawa hukumomin tsaro akan ƙoƙarin da sukayi gurin kuɓutar da Yara Ƴan Makarantar Kimiya da Fasaha na Ƙanƙara.
Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da Jihohi dasu tabbatar ana hukunta masu aikata miyagun ayyuka sabida ya zama darasi ga saura, kuskure ne barin su batare da an hukunta su ba.
Majalisar tayi kira ga Al’umma da Ƙungiyoyi dasu cigaba da bada gudumuwa don Samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
Shugaba Na Ƙasa
Dr. Engr Harris HM Jibril
19/12/2020