Kasuwanci

Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN tayi watsi da karin farashin mai, ta umarci mambobin su siyar akan N163 / ltr.

Spread the love

Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN, ta ce ba ta samu wata sanarwa a hukumance kan karin kudin mai ba, inda ta umarci mambobinta da su yi watsi da karin farashin.

Shugaban kungiyar IPMAN reshen jihar Kano, Bashir Dan-Malam, yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a, ya umarci mambobinsa da su ci gaba da sayar da lita a kan N163.

A cewarsa, a duk lokacin da aka samu karin mai a kasar, masu ruwa da tsaki zasu sanar da shugabannin IPMAN.

Don haka, ya bukaci jama’a da kada su firgita saboda kungiyar ba ta da niyyar sanya mutane cikin wahala.

Mista Dan-Malam ya ce shugabancin kungiyar ta IPMAN ya tuntubi masu ruwa da tsaki a harkar man fetur tare da sanar da su cewa babu irin wannan shawarar.

Shugaban na IPMAN ya kara jaddada cewa Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPC na da isasshen mai don rarrabawa a duk fadin kasar, inda ya bukaci jama’a da su guji sayan mai tsada.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button