Rahotanni
Akwai Yiwuwar A kara Rage Kudin Man Fetir a Najeriya Sakamakon Faduwar Farashin Man Fetir a Kasuwar Duniya….

Ahmed T. Adam Bagas
Hukumar kula da farashin albarkatun man fetur, PPPRA ta bayyana cewa akwai yiyuwar sake kara ko rage farashin man Fetur din nan gaba.
Shugaban hukumar,Abdulkadir Saidu ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya kara da cewa yanayin kasuwane zai bada damar saka rashi sama ko kasa da abinda ake sayen man a yanzu.
Ya kara da cewa suna kokarin hada gwiwa da babban bankin Najeriya, CBN dan ganin cewa ya samar da dala a farashin gwamnati ga dillalan man.
Ya kuma ce nan gaba lokaci zuwa lokaci zasu ci gaba da lura da yanda kasuwar Man fetur din take dan fitar da farashin da za’a sai da Man Fetir Din.