Kasuwanci
Akwai Yiwuwar Ba Za Bude Kasuwannin Kaduna A Gobe Ba, Saboda Injinan Feshin Magani Sun Ki Tashi.
Rototannin da muke samu daga jihar Kaduna na cewa injinan feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka wandanda za ayi amfani da su wajen feshin Kasuwannin jihar sun ki tashi, wanda kuma hakan zai iya sawa a daga bude Kasuwannin daga gobe Alhamis zuwa jibi Juma’a.
Idan baku manta ba a jiya Talata ne gwamnatin Jihar ta Kaduna tace zata bude kasuwannin jihar a gobe Alhamis.
Gwamnatin ta ce ya zama wajibi’yan Kasuwa su kikaye dokar saka takun-kumin rufe baki da hanci, da kuma wanke hannu kafin a shiga kasuwar.
Haka zalika gwamnatin ta ce zata sa ayi feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka don tabbatar kiwon lafiyar jama’ar Jihar.
Sai dai kuma har yanzu gwamnatin jihar bata ce Komai ba kan batun kin tashin injinan feshin.
Daga Muktar Onelove Kaduna.