Labarai
Akwai Yiyuwar Shugaba Buhari Ya Yiwa Majalisar Ministoci Dana shuwagabannin Tsaro Garambawul.
Daga Comr Yaseer Alhassan
Rahotanni daga fadar shugaban kasa na cewa shugaban na shirin yin canje-canje a majalisarsa ta Ministoci.
Shugaban zai yi canjinne nan da watan Octoba, kamar yanda wata majiya daga fadar shugaban ta bayyanawa The Nation.
Yawanci canjin zai shafi kinistocin da aka samesu da wata harkallah ne da kuma wanda ake zargi da cin hanci, kamar yanda majiyar ta bayyana.
Majiyar tace tuni har wasu daga cikin Ministocin sun fara neman kama kafa da wasu na kusa da shugaban kasar dan samu a sake nadasu.