Akwi Tambayoyin Da Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Da Jami’an Tsaro Su Amsa~Martanin Dattawan Arewa Kan Hare-haren Da Ake Kaiwa Gwamna Zulum Na Borno.
Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta yi Allah wadai akan yadda ake kaiwa gwamnan jihar Borno Ferfesa Babagana Umara Zulum hare-hare, ta ce bai kamata ace ma boko haram ta fi karfin gwamnatin Najeriya ba.
Kuma akwai amsoshin da ya kamata gwamnatin tarayyar Najeriya da jami’an tsaro ace sun amsa game da abubuwan da suke faruwa na hare-haren boko haram a arewa maso gabashin Najeriya da kuma yadda ake kaiwa Gwamna Zulum hari.
Kungiyar ta kara da cewa babu dadin jin wasu ababen da suke faruwa kam, sannan kuma ta ce aikin da gwamnati, da jami’an tsaro ke yi wajen yakar boko haram bata gamsu dashi ba.
Wanda a jiya da yamma ma dai an sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum din hari baya ga wanda aka kai Masa a kasa da awanni 48 a hanyar su ta shiga garin Baga, inda maharan suka kashe akalla mutane 20 ciki kuwa harda jami’an tsaro da suke rakiyar tawagar Gwamnan.
Daga Bappah Haruna Bajoga.