Bazan taɓa dena aure ina hayayyafa ba, har sai ranar da mutuwa tazo min — Inji mutumin daya auri mata 16, kuma yake da ƴaƴan 151.

Mutumin mai suna Misheck Nyandoro ɗan ƙasar Zimbabwe ne, anyi ittifaƙin cewa yanzu haka yana da mata guda goma sha shida, tare da zunzurutun ƴaƴa har guda goma ɗari da hamsin da ɗaya.

To amma duk da haka yace atafau, shi baida lokacin da zai dena aurace auracen. Nyandoro ya tabbatar da cewa, yanzu haka yana shirye shiryen ƙara aure na goma sha bakwai ne, domin ƴaƴan sa guda 151 su ƙaru.

“Auren nan nawa na ɗauke shi a matsayin wani abu ne mai kama da kwangila . Wannan auren na mata fiye da ɗaya aiki ne da na fara tun a shekarar 1983 kuma zai ƙare ne kawai idan na mutu. Ma’ana duk lokacin da mutuwa ta kawo cafke Ni, to shine dalilin kawai da zaisa na daina aure da haihuwar yara.

“Ina shirin daukar matata ta 17 a wannan lokacin na hunturu kuma tuni an fara aiwatar da ka’idoji.

“Ya kuma bayyana auren mata fiye da ɗaya a matsayin wata harƙalla wadda take kawo masa abin arziki iri iri kasancewar yana karbar kuɗi da kyautatawa a koda yaushe daga ƴaƴan sa da kuma surukan sa. Nyandoro ya kuma yi iƙirarin cewa yammacin Turai yana da babban aiki don rage yawan mutanen Afirka kuma yana adawa da hakan.Ya ƙara da cewa:

“Ban daina haihuwa ba har yau, sama ita ce iyaka ta. Bazan daina yin aure ba, in Allah Ya yarda, zan auri mata kamar guda 100 watakila sai nakai har yara 1000.

“Yammacin Turai suna da da babban aiki don rage yawan mutanen Afirka kuma ina adawa da hakan. Ni tsohon soja ne, Gwamnati ce ke biyan kuɗin komai na ƴaƴana. Ba ni da matsala.

Mutumin mai auren mata fiye da ɗaya kuma ya ƙara da cewa rayuwa na bashi sukari da daɗi, domin yace ko aiki baya zuwa sai dai ya zauna a rumfar da yake ciyar da dukkan matansa 16 waɗanda suke shirya masa abinci daban-daban don ya ci. Nyandoro ya ce kawai yana zaɓar mai daɗi ne yaci, ragowar kuma ya jefar gefe.Nyandoro yace:

“Kowace mace tana ƙoƙarin dafa abinci mafi kyawu a kowacce rana ta Allah, saboda ka’ida ta ita ce kawai in ci mai daɗi. Kowace mace tana yin biyayya ga wannan dokar kuma bata jin haushi idan na mayar mata da dafafaffen abincin nata.”

Nyandoro yace baya shan kuma wani magani domin ƙarin ƙarfin maza saboda lafiyarsa.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *