Daga karshe dai Mijin Aljana ya karyata kansa, ya ce yana kwarara karya ne domin ya sami kudi.

Mutumin da yayi ikirarin cewa ya auri Aljana Malam Ahmad Ali Kofar Na’isa ya karyata kansa yayin zaman muhawara da akayi dashi da malaman Kano.

Idan baku manta ba a kwanakin baya Dattijon Mai suna Ali Ahmad Kofar Na’isa ya fito ya bayyanawa manema labarai cewa yana da mata Aljana wadda suka shafe shekaru da ita a matsayin miji da Mata, har ma yacigaba da cewa sun haifi ‘ya’ya guda hudu da ita, kuma duka Aljanu ne.

A wata muhawara da hukumar kula da harkokin addini ta jihar Kano ta shirya tsakanin Dattijo Ahmad Ali Kofar Na’isa da Malaman jihar Kano, Dattijon ya ce a zahirin gaskiya duka wannan magan-ganun da ya fada zuki ta malle ne, ya yi hakan ne domin mutane surika zuwa suna siyan Magunguna a wajensa shi kuma yana karbe musu ‘yan kuɗaɗensu, amma babu wani aure tsakaninsa da Aljana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *