Al'adu

Mijina Ya Yi Ƙoƙarin Kasheni, Ya Shaƙeni Da Nufin Ya Kasheni — In Ji Wata Mata Ma’aikaciyar Gwamnati.

Spread the love

Wata ma’aikaciyar gwamnati, Misis Esther Anaagu, ta maka mijinta Emmanuel, a gaban wata kotun al’adu da ke Jikwoyi, Abuja, babban birnin tarayya (FCT), bisa yunkurin kashe ta.

Mai shigar da karar, wadda ke zaune a Orozo, Abuja, a cikin karar saki, ta ce: “Ba zan iya ci gaba da zama karkashin wannan mutumin ba, yana so ya kashe ni.

“Ya yi ƙoƙari ya shake ni har na mutu a wata rigima da mukai, amma na yi nasarar tserewa.

“Daga baya ya ce abin da ya yi ba da gangan ba ne, cewa wani mugun nufi gare shi.

“Ina rokon kotu ta ‘yanto ni daga hannun wannan mutumi, ta raba aurenmu,” in ji ta.

Alkalin kotun, Labaran Gusau, ya shawarci ma’auratan da su binciko duk hanyoyin da za a bi domin sasantawa, ko dan yaran da suka haifa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button