Labarai

Alhassan ado Doguwa ya janye daga takarar Neman Shugabancin Majalisar wakilan Nageriya.

Spread the love

A wani al’amari mai cike da ban mamaki, ‘yan takara uku da ke neman Shugaban Majalisar Wakilai ta 10 mai jiran gado, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhassan Ado Doguwa, Abdulraheem Olawuyi da Abubakar Makki Yelleman sun fice daga takarar tare da goyon bayan dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Tajuddeen Abbas.

Sun bayyana matakin nasu ne a taron hadin gwiwa- na-10 da aka yi a Abuja a daren Laraba.

Taron ya samu halartar shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila da dan takarar shugaban majalisar dattawa na 10, Sanata Godswill Akpabio.

Doguwa wanda ya yi magana a madadin sauran ‘yan takarar biyu ya ce, sun yanke shawarar ficewa ne saboda zabin jam’iyyar APC na mutunta Jam’iyyar tare da yin daidai da wanda ake so a kujerar Shugaban Majalisar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button