Ali Nuhu ya Riga kowa Shiga Zanga Zangar #EndInsecurity
Jama’a da dama na zargin Ali Nuhu da Rashin Shiga Sahun masu Zanga Zangar Endinsecuri Wacce matasan Arewa ke gudanarwa yanzu Haka, Wannan magana ba Gaskiya bace domin kuwa yau kwana hudu kenan da jarumin ya Shiga Sahun ‘yan Zanga Zangar ta hanyar fitar da sanarwar a Shafukansa na sada zumuntar Zamani Abinda Jama’a Basu fahimta ba shine ita wannan Zanga Zangar ba Dole bane sai ka fito a.a ko a kafar sada zumuntar Zamani kana iya Shiga musamman mutun kamar Ali Nuhu dayake da karfi a Shafukan Yanar Gizo…
Kwana Hudu da suka huce Jarumin yayi Wannan Sanarwa kamar Haka..
Zanga-zangar mai taken #EndInsecurityNow za ta fara gudana ne a gobe Alhamis 15 ga watan Oktoba 2020 a dukkan jihohin Arewacin Nijeriya.
Don haka wannan kungiya ta i kira ga duk wani dan Arewa mai kishin kawo karshen ta’addanci da kashe-kashen rayukan al’umma ya fara rubuce-rubuce a kafafen sada zumuntar zamani yana kiraye-kiraye ga gwamnati ta kawo karshen matsalar tsaro a yankin Arewa da Hashtag #EndInsecurityNow.
Kennan ali Nuhu shima ya shigo Sahun…
M inuwa MH