Labarai

Aliyu Atiku Abubakar da Fatima Nuhu Ribadu Zasu Angwance Ranar azabar

Spread the love

An tabbatar da cewa shahararren dan siyasar nan na APC kuma tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Nuhu Ribadu zai shirya gagarumin bikin aure domin kyakkyawar ‘yarsa, Fatima Nuhu Ribadu, Wanda za’ayi a Ranar Asabar, 3 ga Oktoba, a Abuja Wanda zata auri Alliyu Atiku Abubakar, daya daga cikin ‘ya’yan tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, zai angwance da Fatima Nuhu Ribadu. Za a fara bikin aure a ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, Wanda Kuma za’a Daura auren a ranar Asabar, 3 ga Oktoba.

Fatima Ribadu ta kammala karatun ta ne a kwalejin horar da ‘yan asalin kasa ta Nijeriya da ke Abuja kafin ta yi tafiya zuwa kasashen waje don ci gaba da karatun ta.
Tana ɗaya daga cikin hazikan ‘yan matan Arewa. Aliyu kuma ya kasance na Musa kusa da mahaifinsa,
Atiku Abubakar. Aliyu dan Hajja ne, kanwa ga Lamido na Adamawa, Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button