Labarai

Alkalai uku suna wulakanta ra’ayoyin milyoyin ‘yan Nageriya ta Hanyar Yanke danyen hukunci dole mu kawo karshen wannan ~Cewar Obasonja.

Spread the love

A baya-bayan nan dai an kori wasu gwamnoni uku na jam’iyyar adawa a wasu hukunce-hukuncen da alkalan kotun daukaka kara suka yanke.

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana hukuncin da alkalan Najeriya suka yanke a matsayin hukunci na son zuciya” kan rikicin zabe, yana mai cewa bai kamata alkalai uku zuwa biyar su soke hukuncin da miliyoyin masu kada kuri’a suka yanke a lokacin zabe ba.

Obasanjo ya bayyana ikon da aka baiwa wasu alkalai a matsayin wanda sam ba za a amince da shi ba.

Da alama dai tsohon shugaban kasar yana magana ne dangane da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a baya-bayan nan kan rikicin zabe da ya taso a zaben 2023 a kasar.

A baya-bayan nan dai an kori wasu gwamnoni uku na jam’iyyar adawa a wasu hukunce-hukuncen da alkalan kotun daukaka kara suka yanke.

Gwamnonin da abin ya shafa sun hada da Dauda Lawal na jihar Zamfara, Abba Yusuf na Kano, da Caleb Mutfwang na jihar Filato.

Hukunce-hukuncen sun haifar da martani, wanda hakan ya sa bangaren shari’a ya fi fuskantar barazana.

Da yake jawabi a wani babban taron tuntuba kan Rethinking Western Liberal Democracy in Africa da aka gudanar a Green Resort Legacy, Olusegun Obasanjo Presidential Library, Abeokuta, jihar Ogun, Obasanjo ya caccaki “lalacewar Cathedral” da alkalai suka yi.

Ya ce, “Na yi imanin kowace irin tsarin dimokuradiyya da muke da shi ko kowane irin tsarin gwamnati da muke da shi, bai kamata maza uku ko hudu a bangaren shari’a su yi watsi da shawarar da mutune miliyoyin da suka kada kuri’a ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button