Allah Ɗaya Gari Bamban: Sabuwar Shekarar 2013 Ta Kama A Ƙasar Ethiopia.
A yau al’ummar ƙasar Ethiopia a bisa tsarin kalandarsu suka shiga sabuwar shekarar 2013. Al’ummar ƙasar sun fara gudanar da shagulguna daban-daban domin nuna farin cikinsu da sabuwar shekarar data kama. Saɓanin sauran ƙasashen duniya da su ke cikin shekarar 2020.
Mutane da yawa kansu yana daure kuma suna mamaki idan aka cewa sai yanzu shekarar 2013 ta kama a ƙasar Ethiopia , to amma ga dalilii:
Ƙasar Ethiopia (Habasha) turawa ba su yi mata mulkin mallaka ba dan haka komai na su ya sha bamban dana sauran ƙasashen duniya misali :
-Tsarin agogonsu : A bisa tsarin agogon ƙasashenmu ƙarfe 12:00Am shi ne tsakar dare amma su kuma ƙarfe 6:00Am shi ne tsakar dare a wurinsu
-Haruffansu(Alphabets): Suna amfani da haruffa guda 345 a rubutunsu
-Harshen da suke amfani dashi a hukumance (Official language): Harshensu na gida shi ne yaren da su ke amfani da shi a makarartu ko wajan gudanar da harkokin da suka jiɓinci gwamnati. Da sauransu
- Tarin kalandarsu: A ƙasar Habasha suna da watanni 13 sannan kowanne wata yana kwana 30 cif-cif idan ban da na ƙarshe daya ke kwana 6 ko biyar. Sannan a tsarin kalandarsu shekara tana da kwana 365 da awanni 6 da second 24. Sauran ƙasashen duniya suna murnar zagayowar sabuwar shekara duk ranar 1 ga watan Janairu na kowacce shekara amma a ƙasar Ethiopia sabuwar shekara tana kamawa a ranar 11 September.
Bugu da ƙari, daidai cutar covid19 a ƙasar Ethiopia suna kiranta da covid12.
* Ga suunayen watanni a tsarin kalandar ƙasar Ehiopia
1- Meskerem- Wanda yake kamawa a ranar 11 September a tsarin kalandarmu (gregorian calendar)
2- Tikemet – Wanda ya ke kamawa a ranar 11 October
3- Hidar – Wanda ya ke kamawa a ranar 10 November
4- Tahesas- Wanda ya ke kamawa a ranar 10 December
5- Tir – Wanda ya ke kamawa a ranar 9 January
6- Yekatit – Wanda ya ke kamawa a ranar 8 February
7-Megabit – Wanda ya ke kamawa a ranar 10 March
8- Miyata- Wanda ya ke kamawa a ranar 9 April
9- Ginbot – Wanda ya ke kamawa a ranar 9 May
10- Sene- Wanda ya ke kamawa a ranar 8 June
11- Hamble – Wanda ya ke kamawa a ranar 8 July
12- Nehase- Wanda ya ke kamawa a ranar 7 August
13- Pagume – Wanda ya ke kamawa a ranar 6 September
* Ga sunayen ire-iren kalandojin da ake amfani dasu a duniya:
1- Gregorian Calendar (wacce muke amfani da ita a hukumance)
2- Julian Calendar
3- Hindu Calendar
4- Buddhist Calendar
5- Islamic Calendar (wacce muke amfani da ita a musulunce)
6-Ethiopian Callendar
7-Chines Calendar