Siyasa
Allah Sarki: Shima Gwamna Zulum Sun Saki Labarin Karya Akansa.
Gwamna Zulum ya karyata wani labari da ake yadawa a kofofin sada zumunta, wanda suke cewa gwamnan ya ce “Ba zan taba lalata hotona ta hanyar zuwa Jihar Edo don shugabantar kamfen ba, bayan ganin duk abin da Oshiomhole ya ce game da shi a 2016.”
Gwamna Babagana Zulum ya ce “Labaran karya ne! Pls kuyi watsi da wannan barna. Bai zo daga wurina ba, kuma ba zai taɓa iya kasancewa daga gareni ba. Ni cikakken dan jam’iyyar APC ne, kuma dari bisa dari ina nuna goyon baya ga duk dan takarar APC ta tsayar a kowane bangare na Najeriya.”
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.