Allah ya kubutar dani daga cutar COVID-19 ne domin kawai na Cigaba da bauta Masa ~Inji Obasonjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, a ranar Asabar ya ce Allah ya ceci ransa ne a yayin barkewar annobar COVID-19 domin ya cigaba da yi masa hidima da Tsawon Rai..
Ya kuma roki ‘yan Nijeriya da suka tsira daga COVID-19 kuma suka Samun Ikon shigowa sabuwar shekarar da su kasance masu godiya ga Allah Kan Wannan jinƙai nasa.
Yayi wannan jawabi ne a wajen taron godiya karo na biyu na kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Ogun (CAN) da aka gudanar a babban dakin karatu na Olusegun Obasanjo, Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Obasonjo yace
Kasancewar kana raye yana bukatar godiya ga Allah.
“Kuma idan Allah ya ba ku wannan alherin don ku ci gaba da zama a duniya, wataƙila da wata manufa be
“Na yi imani dalilin shi ne ku ci gaba da bauta wa Al’umma da kuma Allah.
Hakika “Ba za ku iya zama bayin Allah ba idan ba za ku iya gode masa ba,” in ji shi.
A jawabinsa na maraba, shugaban kungiyar CAN a jihar, Bishop Akin-Akinsanya, ya ce godiyar, wacce ta zama taron shekara-shekara, an tsara ta ne don karrama Obasanjo a matsayin Asiwaju Onigbagbo na jihar Ogun.
Ya bukaci Kiristoci da su nuna godiya ga Allah saboda tsira da sukayi daga cutar COVID-19 da aka yi a Shekarar 2020