Addini

Almajiri ba abin wulakantawa bane

Daga Marubuciya Khadija Garba Sanusi

Kalmar “Almajiri”, kalma ce ta Hausa wacce ta ke nufin ɗalibi. Kuma ta samo asali ne daga kalmar larabci ta “Almuhajir” wacce ta ke nufin mutum mai neman ilimi. Wacce kuma ta samo asali ne bayan hijirar manzon Allah SAW daga birnin makka zuwa madina inda a wannan lokaci ake kiran duk waɗannda su ka bi manzan Allah zuwa madina da sunan “Almuhajirun”. Watau “Masu ƙaura”.

A kasar Hausa kuma, Almajirai na nufin yaro wanda ya bar iyayensa ya fita daga garinsu ko ƙauyensu ya bar ƴan uwa da danginsa ya tafi wani gari, kauye, karkara ko maraya domin neman ilimin addinin musulunci wurin wani malami.

Almajiranci a Arewacin Nageriya ya samo asali ne daga kasar Maiduguri tun bayan kafuwar Addinin Musulunci a cikin ƙarni na 11 kafin shigar wannan tsarin a cikin Daular Usmaniyya bayan Jihadin Shehu Usman dan Fodiyo.

Waɗannan Dauloli sun taimaka wa tsarin matukar gaya

Bayan da turawan mulkin mallaka su ka haɗe kudanci da Arewaci wuri daya a matsayin kasa me suna Nageriya a cikin shekarar 1914, tsarin gudanarwar karatun allo ya samu tsaiko da naƙasu biyo bayan samar da tsarin ilimin karatun Boko.

Samuwar tsarin karatun boko shine matakin farko da ya fara kawo nakasu ko koma baya ga wannan tsarin na almajiranci a kasar Hausa.

Tsarin karatun boko shi ya Raba malaman addinin musulunci da ayyukansu na damar samun aikin koyarwa daga gwamnati saboda ba su da ilimin koyarwa a makarantun Boko. Sannan kuma sai ya kasance Malaman sun rasa dukkan wani tallafi na sarakuna da gwamnati

Almajiri yaro ne da ake fatan ya samu ilimin addini tun daga ƙuruciya ta yadda ilimin zai zame masa mai amfani shi da al’umma a lokacin girma.

A Jiha Kano Wangarawa sune suka fara kafa Makarantar Allo,
Sheik Abdurrahman Zaiti (wanda Yakafa Unguwar Zaitawa) Da Jama’arsa Sune Suka Fara Kafa Makarantar Allo Dan koyar Da Alqur’ani Me Girma a garin Kano.

Wannan Makarantar Aciki Ake Koyan Karatu Rubutu Da kuma Haddace Alqur’ani Me Girma.
Malaman Makarantar Allo Su Suke Rubuta Alqur’ani Da Ka.

Tsarin Makarantar Allo.

Makarantar Allo Guri Ne Me Tsari Sosai Ada,
Asali Iyaye Ne Kan Kai Yara Wanann Makarantar ,
Kuma Yaran Da Ake Kaiwa Sai Sun kai Shekara Bakwai Zuwa Sama Kuma Ana Hadawa Yaro Abinda Zaici Bazaiyi Bara ba, Wanda a Wannan Lokacin Anyiwa Yaro Kaciya. Idan Aka Kai Yaro Shikenan Ya Zama Dan Makaranta Da Ake kira Almajiri.
Wadannan Daliban Kala Biyu Ne :
Akwai Wadanda Suke Kwana.
Akwai wadanda Suke Zuwa Su Dawo Gida Kamar Yanda Yan Boko sukeyi.

LOKUTAN KARATUN ALLO.

A Makarantar Allo Ana Karatu Kusan So Biyar.

  1. Ana Fara Zama Karshen Dare Dab Da Sallar Asubah Har Zuwa Dagawar Hantsi.
  2. Bayan Azahar Idan Akai Sallah.
  3. Sai kuma Bayan Sallah Magariba
  4. Sai kuma Bayan Sallah Isha’i.
    Wadannan Sune Lokutan Da Ake Karatu A Makarantar Allo Ta Asali,
    Dan Haka Yaran Da Kuke Gani A Titi Cikin Tsumma Wasu Cikin Bola ko A Gidan karuwai, Mabarata ne Ba Almajiran Alqur’ani Ba .
    Almajiran Alqur’ani Mutane Masu Nutsuwa Da Basira,
    Duk Abinda Suka Sa A Gaba Da wuri suke Gane shi. Ko kasan Sarkin Kano Na Farko A Daular Fulani Almajiri Ne?
    Ko kasan Alhaji Alasan Dan Tata Almajiri Ne?
    Ko kasan isyaka Rabiu Almajiri Ne?
    Ko Kasan Sheikh Nasiru kabara Almajiri Ne?
    Ko kasan Sheikh Jafar Almariji ne.?

Me Yasa Baa Banbance Mabarata Da Makarantan Alqur’ani?

Tsarin Shugabanci A Makarantar Allo.

Uban Zangaya Shine Shugaba Na Kololuwa wanda kusan Da Sunansa Ake Kiran Makarantar. Misali Ace Tsangayar Malam Wane.

Matakai Na Ɗalibta A Tsangaya.

  1. Ƙolo _ Primary
  2. Titi biri _ Junior Secondary
  3. Gardi Senior Secondary
  4. Alaramma Graduat
  5. Gwani. Doctor
    6.Gangaran Professor.

Masu karatun Alqur’ani mutane ne masu Dogara Da Kansu
Har Akwai saba’oin dasu suka shahara dasu. Misali: Dinkin Wula, Kubta. Da Sauransu.

Me ya hada karatun Alqur’ani Da Bara?

Dalilai da yawa ne Suka Tilastawa Daliban Makarantar Allo yin bara Wanda Insha’Allahu a Rubutuna na gaba zan kawosu Amma kafin nan bara nayi muku matashiya. mutanen kasar Algeria da sukazo karatun Allo Arewa sune suka fara tura dalibansu zuwa gidajen Mutane su barato musu Abinchin da zasuci amatsayinsu na baki Wanda Basu son Kowa ba a gari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button