Alqur’ani Tafarkin Tsira Kashi Na Biyu-Alaramma Sadik Madabo
Alqur’ani Tafarkin Tsira
Kashi Na Biyu
1- A. Guri nawa ake sujuda a Qur’an? B. Wace sura ake sujuda sau biyu? C. Me ake fada a sujudar tilawa?
2- Wata sura ce a duk aya sai da aka maimata Lafzul Jalalah (الله)?
3- A. Surori nawa ne suka fara da (الحمد)? B. Surori nawa ne aka fara su da rantsuwa?
4- A. Sunayen Annabawa nawa Qur’an ya ambata da Qissarsu? B. Kawo sunayen.
5- A. Al-Qur’an ya kawo sunayen dabbobi masu tarin yawa, fadi 10 a ciki. B. Ya zo da sunayen abubuwa da dama, kawo 5 kacal. C. An kawo sunan tufafi da dama, zo da 3 kawai.
7- Wata aya ce aka kawo umarni 2, hani 2, bushara 2 a ciki?
8- A. Wace mace ce aka ambaci sunanta karara a Qur’an? B. Sau nawa aka ambaci sunan?
9- A. Surori nawa ne suka fara da “حروف المقطعة” B. Kawo su.
10- A. Surori nawa ne suka fara da (قل) B. Kawo su
11- Wata Sura ce Annabi (S) yace: Tana korar Shaidan daga gida?
12- Kawo gurare a kalla biyar da aka sunnanta karanta Suratul Ikhlas (Suratut-Tauhid)
13- Wata sura ce in mutum ya haddace ayoyi 10 na farkonta zai tsira daga Dujjal?
14- Wace Sura ce za ta ceci mutum har a yi masa gafara in yana karantawa… Kuma ana karantawa mamaci?
15- Surar da in mutum ya karanta ayoyi biyun karshenta a dare ta isar masa ita ce…
16- Surori biyu da za su tsayawa mutum (Da ceto) ranar Qiyamah sune….
17- A. Wata aya ce da aka saukar Annabi (S) yace: ku sanya ta a ruku’u? B. Wata aya ce da aka saukar yace: ku sanya ta a sujuda?
18- Wasu surori ne Annabi (S) yace: Mai son ya yi duba kamar yana kallon filin Qiyama da idanunsa ya karanta su?
19- Me ake cewa in an karanta: A. Ayar karshe ta Suratul Qiyama? B. Ayar farko ta suratul A’ala? C. Aya ta 74 da ta karshe a Suratul Waqi’a? D. Ayar karshe ta Suratul Haqqat?
20- Yayin da wannan ayar ta Suratul An’am ta sauka, da Allah Ta’ala yace:
“قل هو القادر على أن يبعث عليكم عذابا من فوقكم…..
A. Sai Annabi (S) yace: …….
Sai Allah Ta’ala ya saukar da:
“أو من تحت أرجلكم…….
B. Sai Annabi (S) yace: …….
Sai Allah Ta’ala ya saukar da:
أو يلبسكم شيعا ويذيق بعضكم بأس بعض…….
C. Sai Annabi (S) yace: ……..
Da alamu wanda ya kakkabe tambayoyin yau Zai Iya Samun kyauta.
Mu Hadu a Kashi Na Uku
✍️Rubutawa Da Tsara Tambayoyi: Alaramma Sadik Madabo.
Tacewa Da gabatarwa: Ismail Aliyu Ubale
WhatsApp>08038485677