Alqur'ani Tafarkin Tsira

Alqur’ani Tafarkin Tsira Kashi Na Daya

Spread the love

Alqur’ani Tafarkin Tsira (Kashi Na Daya)

1- Wadanne ne sunayen Al-Qur’an da suka zo a cikin Qur’an?

2- A. Surori nawa ne a Qur’an?
2B. Hizb nawa ne a Qur’an? 2C. Ayoyi nawa ne a Qur’an? 2D. Kalmomi nawa ne a Qur’an?
2E. Harufai nawa ne a Qur’an?

3- A. Surori nawa aka saukar a Makkah?
3B. Surori nawa aka saukar a Madinah?

4- A. Wacce sura ce ba a fara ta da BismiLLah ba?
4B. Wace sura ce ke da BismiLLah biyu?

5- Surori nawa ne masu sunan Annabawa?

6- A. Wacce sura ce tafi ko wacce tsayi a Qur’an?
6B. Wacce sura ce tafi ko wacce gajarta a Qur’an?

7- Suna nawa ne da Suratul Fatiha?

8- Sau nawa aka ambaci Lafzul Jalalah (الله) a Qur’an?

9- Wacce kalma ce ta raba Qur’an gida biyu dai-dai?

10- A. Wacce Surah ce take da kasra guda daya jal?

10B. Kawo suna biyu da ake kiran Surar da shi.

Ku Rubuta Mana Cikakken Sunan Ku tare da Amsar Ku, Dakuma adireshin Email Dinku.

Mu Hadu a Kashi Na Biyu.

️Rubutawa Da Tsara Tambayoyi: Alaramma Sadik Madabo.

Tacewa Da gabatarwa: Ismail Aliyu Ubale
WhatsApp>08038485677

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button