Labarai

Al’ummata Suna Rayuwa Cikin Bala’i, Ka Taimaka Ka Ceto Rayuwarsu Su, Rokon Gwamnan Jihar Neja Ga Shugaba Buhari.

Spread the love

Gwamnan Jihar Neja, Ya Nemi Shugaba Buhari ya Ceto Rayuwar Al’ummarsa.

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya koka wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa mutanen jiharsa na rayuwa cikin bala’i saboda lalacewar tituna da ambaliyar ruwa.

Bello ya bayyana hakan ne a yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar a fadarsa da ke Abuja Jiya Juma’a inda ya nemi gwamnatin tarayya ta kawo ma al’ummar jiharsa dauki don yaye musu damuwar da ke adabar su ta Rashin Hanyoyi mota a fadin Jihar.

Yayin da ya ke magana da ‘yan jarida bayan ganawarsa da shugaban kasar, ya ce rashin kyawun titunan gwamnatin tarayya yana barazana ga rayuwar mutane kuma hakan na iya zama silar Hana tafiye tafiye ga Al’ummarsa.

Ko a Ranar Yancin kai Na Wannan Shekarar Gwamna Bello, ya yi rangadin gani da Ido a Hanyar Minna zuwa Suleja, Inda Gwamnan yaga halinda matafiya ke ciki a hanyar.

Ko a makon da ya gabata Mai martaba Sarkin Bidda kuma shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Neja, Alhaji. Dr Yahaya Abubakar Etsu Nupe, Ya ziyarci Ministan Aiyuka Na Kasa, Hon. Babatunde Fashola a Abuja, Domin Neman Gwamnatin Tarayya ta waiwaiyi Aikin Hanyar da tahada Minna zuwa Bida, dake Jihar.

Bello, ya kuma koka kan yadda ambaliyar ruwa a bana ta lalata filaye masu yawa musamman gonakin rake a jihar. Hakan yasa ya yi kira ga shugaban kasar ya taimakawa manoman jihar da ambaliyar ruwan ya shafa.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button