Rahotanni

Amatsayin injiniya dan Jihar kano Abba Gida Gida ya rubuta Wasika ga Kamfanin da ya Gina Gadar kofar Nasarawa..

Spread the love

Mai girma tsohon Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba K. Yusuf ya rubutawa Kamfanin TEC wanda shi ne yayi kwangilar aikin Gadar sama ta Ƙofar Nasarawa wasika, inda ya bukaci da suyi bincike tare da yi masa ƙarin bayani akan inganci tare da yayewa jama’a fargaba a kan gadar.

Rahotanni sun tabbatar da Cewa Gadar ta kofar Nasarawa na Nan daram kalau Kamar yadda Kamfanin ya sheda

Kwamfanin dai ya bayarda garantin Shekaru dari ne da zummar idan wani Abu ya Sami Gadar to Lallai a tuntuɓe su.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje tace da yiwuwar a rushe gadar ta Kofar Nasarawa saboda ta gano cewa an yi aikin gaggawa yayin ginin gadar, wanda hakan yasa wani sashe na gadar ba a yi aiki mai inganci ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button