Labarai

Amurka Ta Gano Ba China Ce Ta Kirkiri Cutar Corona Virus Ba…

Spread the love

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Hukumomin leken asirin Amuka sun ce sun gano cewa ba dan Adam ne ya kirkiri cutar Covid-19 ba sannan kuma ba sauya kwayar halitta aka yi ba, a wani bayanin farko da Hukumomin suka fitar.

Sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike kan ko cutar na da alaka da yin hulda da dabbobi ko kuma wani abu da ya faru a wani dakin gwaji na kasar China.

Sai dai sun yi watsi da labarin da ake yadawa cewa China ce ta kirkiri cutar sannan ta yada wa duniya.

Idan baku manta ba Shugaba Donald Trump ya sha yin yakin cacar baki da China game da asalin annobar da ta lakume ran fiye da mutum dubu 200 a duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button