Amurka Zata Kaddamar Da Hare-hare 1,000 Akan Iran ~ Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Talata, ya sha alwashin kai wa Iran hari idan ta rama kisan da aka yiwa Maj. -Gen., Qassem Soleimani.
Trump, ya ambaci hakan a wata sanarwa ga manema labarai, ya yi iƙirarin cewa Gwamnatin Iran na iya shirin ramuwar gayya saboda mutuwar shugaban soja.
“A cewar rahotanni na manema labarai, Iran na iya shirin kisan kai, ko kuma wani hari, kan Amurka a matsayin ramuwar gayya ga kisan shugaban sojanta Soleimani, wanda aka aiwatar don shirinsa na kai hari nan gaba, kisan Sojojin Amurka, da kuma mutuwar da wahala da aka haifar tsawon shekaru.
“Duk wani harin da Iran za ta kaiwa Amurka, ko ta wace fuska, za ta gamu da harin da za ta kai wa Iran din wanda zai ninka har sau 1,000 a girma !,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata.
THE WHISTLER ta ruwaito cewa Soleimani, wanda shi ne shugaban fitattun Quds Force kuma matattarar tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya, an kashe shi a wani harin jirgin saman Amurka tare da mai ba shi shawara, Abu Mahdi al-Muhandis, a filin jirgin saman Baghdad da ke Iraki.
“A bisa umarnin shugaban kasa, sojojin na Amurka sun dauki matakin kare kai don kare ma’aikatan Amurka da ke kasashen waje ta hanyar kashe Qassem Soleimani.
“Wannan kisan an yi shi ne domin dakile shirye-shiryen kai harin Iran a nan gaba,” in ji gwamnatin Amurka a cikin wata sanarwa.
Har yanzu gwamnatin Iran ba ta mayar da martani kan ikirarin na Amurka ba har zuwa lokacin da muka hada wannan rahoton.
A halin yanzu, Ministan Harkokin Wajen Iran, Javad Zarif, ya yi tir da yarjejeniyar zaman lafiya da ke gudana tsakanin Isra’ila da wasu kasashen Larabawa.
Zarif ya jaddada cewa Gwamnatin Trump na amfani da hakan don samun tagomashi kafin zaben shugaban kasa mai zuwa a ranar 3 ga Nuwamba.