Kasashen Ketare

Amuruka Na Fuskantar Barazana….

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Shugaban Hukumar yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurika Dr. Anthony Fauci yace Kasar Na fuskantar Babbar Barazana daga Corona Virus.

Fauci yayi wannan jawabi ne a Wani taro da aka Gudanar a Gidan Gwamnatin kasar White Hause, yace Ansamu Mutane dubu 40.173 da suka kamu da Cutar a Rana Guda, hakan Ba karamar barazana bace ga Al’ummar Kasar Inji Shi.

Fauci yace Jahohi 16 ne a Kasar ke fama da Cutar Yanzu Haka.

Alkaluman Jami’ar Johns Hopkins tace Kawo Yanzu Mutane sama da Miliyan 2 da Dubu dari 4 ne ke Dauke da Cutar a Kasar, Yayinda Tayi Ajalin Mutane dubu 125. A Kasar.

Sai dai Mataimakin Shugaban kasar Amurika Mike Pence yace Akwai Bukatar a Hada Karfi da Karfe da kowa a Kasar ayi kokarin Dakile Cutar a Kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button