An Amince Yaci Gaba da Mulki Har Karshen Rayuwar sa.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
A Ranar Juma’ar da ta gabata ne Majalisar Jamhuriyar Chadi ta Kyara Dokar Kasar Na Baiwa Shugaban Kasar Mukamin Field Marshal daga Mukamin Genaral.
Mukamin Field Marshal Dai Shi ne Kololuwa a Aikin Soja, Majalisar Kasar Ta ce Ta Bashi wannan Mukamine Na Field Marshal domin yaci Gaba da Shugaban tar Kasar Har Karshen Rayuwarsa Domin Jajircewarsa Wajen Nemawa Kasar Da Yan Kasar Martaba.
Majalisar Tace ya chancanci Wannan Matsayin duba da Yadda ya Jagoranci Rundunar Sojin Kasar Zuwa Filin daga Suka Kakkabe Yan Ta’addan da suka Addabi Kasar.
Sannan Idrissa Deby Into Ya Tura Sojoji Kasashen Nigeria da Mali Domin kai Musu Dauki.
Sai Dai Ba Shi ne Kadai Ya fara Ruke Irin wannan Babban Mukamin na Soja ba, Wa `Yan da Suka Ruke Irin wannan Mukamin A Sassan Duniya Sun Hada da Shuwagaban Ni Kamar Haka:-
Mohsmed Hussein – Masar
Idi Amin Dada – Uganda
Jean-Bedel Bokassa – Jamhuriyyar Dimokradiyyar Africa ta Tsakiya.
Da dai Sauran Su.