Siyasa

An Bukaci Shugaba Buhari da El-Rufa’i Suyi Murabus.

Spread the love

Wata kungiya mai fafutukar Tabbatar da Dimokuradiyya, a Najeriya tayi kira da Kakkauras Murya kan Gwamnan Jahar Kaduna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suyi Murabus da Karagar Mulki.

A wata sanarwa da mai magana da Kungiyar Mr Deji Adeyanju ya Fitar yau Litinin, Yace Yan Ta’adda Sun Addabi Kudancin Kaduna Inda suke ta kashe Mutane amma Gwamnati tayi Shuru ta zuba Ido bata yi abinda ya dace Ba Inji Shi.

Adeyanju yace Kare Rayuka da Dukiyoyin Al’umma ya ratane a wuyan Gwamnati, sai Dai abin Takaici Ana Zubda Jinin Al’ummar Kudancin Kaduna Gwamnatin Tarayya da ta Jaha Sunyi Shuru, Fulani Makiyaya suna Kashe Mutane Inji Mr. Deji.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button