An Bukaci Sifeton ‘Yan Sanda Ya Kori Ibrahim Magu daga Aikin ‘Yan Sanda.
A Jiya Alhamis ne Kwamitin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kafa kan Magu ya bada rahoton da ya tattara.
Idan Baku manta Ba a watan da ya gabata ne Aka zargi Shugaban Riko Na Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa Ta’annati da Zagon Kasa Ibrahim Mustapah Magu, da Cin Hanci da Rashawa. Wanda hakan yayi sanadiyar Jami’an Tsaron DSS suka kamashi daga Karshe Shugaba Buhari ya Sallameshi daga Hukumar ta EFCC.
Buhari ya kafa Kwamitin ne Domin a gudanar da bincike domin Tabbatar da Zargin da akewa Magun, Kwamitin wanda mai Shari’a Ayo Salami yake Jagoranta Shugaba Buhari ya Basu adadin Kwanaki 45 Su kawo masa Rahoto.
A jiya Alhamis ne kwamitin ya cika adadin kwanakin Sun gabatar wa Buhari Irin Sakamakon da suka Tattara Kuma A zarge zarge guda 12 da akewa Magu ya kasa kare kansa Daga duk kan zargin da ake masa Inji Kwamitin.
Justice Salami ya Bukaci Shugaba Buhari da ya kara musu Wa’adin Wasu kwanakin Domin Cigaba da Gudanar da Bincike Akan Magun.
Bayan Gabatar da wannan Sakamakon Kwamitin ne Kwamitin Suka Bukaci, Shugaban ‘Yan Sanda Na Kasa IG. Muhammad Adamu da Ya kori Ibrahim Mustapah Magu daga Aikin ‘Yan Sanda Kuma a Gurfanar dashi gaban Kuliya domin ya Fuskanci Shara’a kan Abin da ya Aikata a Ofishinsa.
A zarge Zargen da akewa Ibrahim Magu Sun hada da Sace, Manyan Gidaje Na Alfarma Har Guda 321, Jiragen Ruwa, da Makudan Kudade, Sannan ya Kulle Asusun ‘Yan Kasuwa ba bisa ka’idaba sannan ya Ki Biyayya ga Umarnin Kotu a lokuta da Dama kuma Ya ki Biyayya ga Ma’aikatan Hukumar Shara’a Ta kasa.
Kuma Magu Shine wanda Shugaban Kasa ya bashi Rikon Kwarya har Shekaru 5 wanda hakan ya sabawa dokar kasa, a dokar kasa ana bada rikon Kwarya ne Na Watanni 6 kacal.
Ko a Shekaran jiya wani Dan kasuwa ya Gabatarwa da Kwamitin Wani faifan Bidiyo da yake Nuna Ma’aikatan EFCC ke Tilastawa Dan kasuwar Ya basu miliyan 75 ko su bata masa Suna.
Ahmed T. Adam Bagas