Tsaro

An cafke Dan sanda da Soja suna fashi da makami.

An kama wani sabon dansanda mai suna David Friday, wanda ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Olofin a karamar hukumar Idanre, da laifin fashi da makami.

An kama David tare da wani soja da ke aiki a 32 Artillery Brigade, Nigerian Army, Owena Cantonment, Innocent Victor.

Kwamishinan ‘yan sanda na Ondo, Bolaji Salami, wanda ya gabatar da wadanda ake zargin ga Manema Labarai, ya ce David ya saci babur a wurin da yake aiki.

Salami ya ce, “An kama shi ya hada baki da wani soja don yi wa wasu mutane fashi da adda. Mun gabatar dasu kuma wadanda abin ya shafa sun gano su. Da zaran mun gama binciken mu, za mu gurfanar da su a gaban kotu. Inji Shi.

Sojan ya musanta cewa yana da hannu a cikin zargin, yana mai cewa ya koma inda lamarin ya faru.

Sauran wadanda aka gurfanar sun hada da Wasiu Lateef, wanda ake zargi da lalata matashi a wani gida da ba a kammala ba a kauyen Lapanu da kuma wani da ake zargi da yin garkuwa da matashi, Bello Ali, wanda ya kasa bayanin abin da yake yi a wani daji da ke tsakanin Uso da Ogbese.

Hakanan, an gabatar da wani Desmond Ikechukwu, wanda ya yi shigar soja domin ya tsoratar da jama’a, shi ma an gabatar da Shi gaban ‘Yan Jarida.

Ahmed T. Adam Bagas✍️

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button