Labarai

An Cinye kudin Lauyoyi An Kuma Kori alkali daga Kotu a jihar Nasarawa.

Spread the love

A jihar Nasarawa An canjawa wani alkalin Kotun Upper Area Court 1 wajen aiki Sakamakon zargin Cewa alkalin ba zai yi Abinda ake so ba, na bin ra’ayin wasu jiga jigan Gwamnatin jihar Kan zargin halllakar da dukiyar lauyoyi Alkalin Mai suna Tijjani Abubakar an canza Masa wajen aiki ne daga Garin lafiya babban Birnin jihar Nasarawa Zuwa karamar hukumar Keana dake jihar Nasarawan.

A Ranar 14 ga wannan watan da muke ciki ne dai alkalin ya bayarda umarnin a kamo babban ma’aji (Accounter Genaral) na jihar Wato Zaka El Yakubu Amma Koda Ma’aikacin Kotun ya Isa Ofishin Akawuntan basu riskeshi ba sai dai a Lokacin da akawuntan ya samu Labarin cewa anzo nemansa daga kotu sai yayi sauri ya garzawa Zuwa Ofishin abokinsa Sani Ahmad wato babban Mai shigar da umarni Lauyan Gwamnatin jihar Nasarawa domin neman tallafinsa Kan Al’ummarin, Lamarin da yasa Jiga jigan Ma’aikatar shari’a Suka taru Suka Kuma zauna sai Suka Kira dan Aiken Kotun suna tambayarsa cewa waye ya bashi umarnin Kama Akawunta? Sai shi Kuma Yace masu alkalinsa Tijjani Abubakar ne ya tabbatar da takardar kamun tare da bashi umarni…

Lamarin daya fusata Rijistaran jihar ya Kuma tabbatar da Cewa Lallai zasu canzawa alkalin wajen aiki, Haka kuwa Nan take ba tare da 6ata Lokaci ba sai Suka Fara shirye shirye Wanda daga karshen Suka canjawa alkalin wajen aiki daga Lafiya Zuwa Garin Keana bayan sun karbe duk wata shedar shigar da Kara ko umarnin Kamu Mai dauke da tambarin amincewar kotu…

A Ranar 14 ga wannan watan ne dai Kungiyar Ma’aikatan lauyoyin Nageriya Law Officers Association of Nigeria (LOAN) ta maka Akawunta Zaka El Yakubu a Kotu bisa zarginsa da karkatar da kudin Karin Albashin da Gwamnatin jihar tayi ga Kungiyar idan baku manta ba wattannin baya da Suka wuce ne dai Gwamna Engr A.A Sule na jihar ta Nasarawa ya aminta da Karin Albashin ga kungiyar ya Kuma rattaba hannu Amma Akawunta Janar din yaki aminta a fitar da kudin Kuma bayan Haka ya rubuta Wasikar mummunan zagi ga Kungiyar ta Lauyoyi Lamarin Dake nuni da Cewa akawuntan yayi Awon Gaba da kudin ko kuma wasu daga cikin kudin Haka Kuma yayi zagi ga Kungiyar Hakan yasa Kungiyar ta yanke hukuncin maka shi a gaban kuliya Kotu domin neman hakinsu..
Lauya Mai kare Kungiyar Mai suna Barista Isah H Na-Laraba shine ya sanar da Jaridar Mikiya Kan Lamarin..

Kawo yanzu MIKIYA ta Kira babban Akawuntan Zaka El Yakubu da Kuma babban Lauyan Sani Ahmad ta waya Kuma mun tura masu Sako ta WhatsApp domin jin ta bakinsu Kan Lamarin Amma haryanzu Babu amsa…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button