Labarai

An Daina Bamu Tallafi, Zamu Koma Fasa Bututun Man Fetur____Inji Tsagerun Niger Delter.

Spread the love

Matasan tsagerun Yankin Niger Delter sun fitar da sanarwar cewa tunda gwamnatin shugaba Buhari ta daina basu tallafi kamar yadda ta yi alkawari abaya to lallai zasu koma fasa bututun man fetur don bazasu juri zama da talauci ba.

Tsagerun Na Niger Delter sukace yau an shafe wata da watanni basuji Alert ba don haka zasu fito suci gaba da fasa bututun man fetur don susami abinda zasu cigaba da ciyar da iyalansu da kuma Kansu.

Suka kara da cewa bazasu zuba ido suna kallo suda arzikin kasar su amma an karkatar da arzikin ga wasu tsirarun yan kasar sunata sace wa sunayin yadda suka ga dama ba saboda suke rike da madafan iko.

Sun jaddada cewa zasu fito zasu ci gaba da fasa bututun man fetur tunda suma yan kasar ne kuma suna da hakki acikin arzikin kasar.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button