Rahotanni

An daure wani Matashi a gidan yari saboda ya tsegumta wa EFCC bayanan karya na wasu maƙudan kuɗaɗe da yace an ɓoye a wani gida

Spread the love

An daure Misbah Ahmed a gidan yari saboda bai wa EFCC bayanan karya

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da wani Misbah Ahmed a gaban mai shari’a Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna bisa tuhuma guda daya da ta shafi yada labaran karya.

Wanda ake tuhumar ya yaudari jami’an Hukumar da cewa an jibge wasu makudan kudade a cikin wani gida da ke rukunin gidaje na Tarayya, Tudun Wada, Jihar Zamfara.

A tuhumar an ce, “Kai, Misbah Ahmad a wani lokaci a cikin watan Yuni, 2023 a Kaduna, da ke karkashin ikon babbar kotun jihar Kaduna da gangan ka ba wani jami’in hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa bayanan karya; cewa akwai wasu makudan kudade na kudin kasar Amurka (USD) na zamba da aka ɓoye a wani gida da ke Federal Housing Low-cost, Tudun Wada Jihar Zamfara, wanda ka san karya ne kuma ka aikata laifin da ya saba wa sashi na 39(39). a) na Hukumar Laifukan Tattalin Arziki da Tattalin Arziki (Establishment) Dokar, 2004 kuma mai hukunci a ƙarƙashin Sashe na 39 (2) (b) na wannan Dokar”.

Misbah Ahmed, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Don haka, lauyan masu shigar da kara, K.S Ogunlade ya bukaci kotu da ta yanke masa hukunci.

Mai shari’a Khobo ya yanke masa hukuncin daurin shekara daya ko kuma tarar N100,000.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button