Kasashen Ketare

An Daure Wani Soja Shekaru 90 Saboda Ya Bindige Kwamandansu Har Lahira.

Spread the love

An Yankewa Wani Soja Hukuncin Daurin Shekaru 90 Saboda Ya Harbe Kwamandansu Har Lahira A Kasar Uganda.

Babbar Kotun Soji ta Kasar Uganda (DCM) da ke zaune a Hedikwatar Brigade ta Marine da ke Gundumar Buliisa a ranar 16 zuwa 18 ga Satumbar 2020, ta yanke wa RA / 241764 Pte Rubagumya Cephas hukuncin daurin shekara tasa’in.

An yanke masa hukunci ne saboda harbi da kuma kashe kwamandansa RA / 205293 lance Corporal Businge Benaerd da yayi a yankin Mulima da ke gundumar Buliisa.

An yake masa hukuncin ne a ƙarƙashin sashi na 188 & 189 na kundin tsarin doka Babi na 120 na dokokin Uganda.

Lauyoyi masu gabatar da kara karkashin jagorancin Maj Gerald Bamwitirsbwe sun fada wa DCM karkashin jagorancin Col Edison Muhanguzi cewa a ranar 27 ga Mayu 2020, Pte Rubagumya Cephas ya bar Mulima ya fice ya tafi garin Hoima don cire albashi, kuma bayan ya dawo da misalin karfe 8:40 na dare ya fara fada da shi kwamanda RA / 205293 lance Corporal Businge Benaerd, kuma daga baya ya samu bindigarsa daga gidan sannan ya umarci Lance Corporal Businge Benaerd da ya zauna, Businge Benaerd ya roki jinkai amma duk a banza, amna sai da ya harbe shi ya kashe shi.

Shaidun masu gabatar da kara RA / 240969 Pte Ochero Joseph da RA / 239190 Pte Chebet Flouk wadanda su ma aka tura su a wannan wurin sun bayyana wa DCM cewa Pte Rubagumya Cephas ya harbe kwamandan su RA / 205293 lance Corporal Businge Benaerd da harsasai goma, jim kadan bayan wata zazzafar mahawara.

Yayin yanke hukuncin RA / 241764 Pte Rubagumya Cephas, Col Edson Muhanguzi ya ce hukuncin ya kamata ya zama gargadi ga dukkan jami’ai na UPDF.

“Wannan hukuncin ya kamata ya zama gargadi ga dukkan hazikan hafsoshi da na Dakarun Sojojin Uganda musamman rundunar Brigade ta Marine,” in ji Shugabar DCM.

An gaya wa mai laifin yana da danar daukaka kara a cikin kwanaki goma sha hudu idan hukuncin ya yi masa tsauri da yawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button