Labarai

An gama Rigimar neman Sarauta yanzu, Ina Kira da ka yi Adalci ga kowa – Saƙon El’rufa’i ga Sarkin Zazzau

Spread the love

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayar da muhimmiyar shawara ga sabon sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
  • El-Rufai ya bukaci Bamalli da ya yi adalci ga kowa domin a yanzu an gama takara
  • Gwamnan ya jadadda cewa ya janyo kowa a jiki daga wadanda suka yi masa mubaya’a har wadanda basu yi masa ba

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi kira ga sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, da ya zama adali ga dukkanin al’umman masarautar.

Gwamnan ya fada ma sarkin cewa gasar neman kujerar ya kare don haka akwai bukatar sarkin ya hada kan mutane, harda wadanda basu yi masa goya masa baya ba.

Gwamna El-Rufai ya bayar da shawarar ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar sarkin a gidan gwamnati yayinda suka kai masa ziyarar godiya a ranar Laraba.

“Rokona shine ka ci gaba da hada kan kowa da kowa, ka ja kowa a jiki, ka koyi darusa daga gogewar mambobin majalisar masarautar Zazzau.

“Domin aiki tare zai kai masarautar Zazzau ga tubalin nasara da ci gaba, zai kawo zaman lafiya da hadin kai. Ina kira ga sarkin da ya zama adali ga kowa. Ga wadanda suka yi masa mubaya’a da wadanda basu yi masa ba saboda gasa ya kare.

“Babban aikin yanzu shine fara hada kan kowa da kowa, cimma nasara da kare martabar wannan masarauta da dukkanmu muke alfahari da ita,” in ji shi.

Da farko, Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya fada ma gwamnan cewa sun zo gidan gwamnati domin mika godiya a kan zabarsa da ya yi a matsayin magajin marigayi sarki Dr Shehu Idris.

Ya ce ba karamin aiki bane saboda gasar da aka fuskanta a lokacin zaben amma ya ba gwamnan tabbacin samun biyayyan masarautar.

Ya kuma fada ma gwamnan cewa akwai wakilan dukkanin daular a tawagarsa wanda hakan ke nufin akwai hadin kai da zaman lafiya a masarautar.

“Saboda haka na yarda cewa mu ahli guda ne kuma bana ganin akwai wani dalili da zai sa a ware kowani daula. Dukkanmu yan uwa ne kuma mun dade a tare. Na rike mukamin Magajin Gari na tsawon shekaru 19 don haka ina da kwarewar da zan yi aiki da kowa,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button