An Gano Gawar Mutum 14 Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Garin Dan Aji Ta Jihar Katsina Kamar Yadda Kabir Nasir Sheme Ya Tabbatar.
A halin yanzu anga gawar mutum 14 da yan ta adda suka kashe jiya a garin Dan’ aji dake Yar’ malamai word, Faskari L G. A. bayan kona musu dukiyoyi da gidajen su
Kabir Nasir sheme ya tabbatar da cewa al ummar karamar hukumar Faskari suna cikin tashin hankalin yan ta adda.
Kabir Nasir sheme yace wani bawan Allah da abun ya rutsa dashi yasamu nasara ya boye, yanaji suna fada cewa, “” sai mun tada duk wani gari daga Nan har Funtua. “
Yakara da cewa jirgin dayake sakin bam din ma ba a wajen da yan ta addan suke yake sakin bam din ba awani guri can yake sakin bam din ba a inda yan ta addan suke ba.
Kabir Nasir sheme yace suna rokon wadanda abun bai shafa ba Ku kara sakasu cikin addu’o inku Allah yakawo karshen wannan iftila’in, Allah yakarbi shahadar wadanda suka rasa ransu, masu raunuka da makamancin hakan Allah ya basu waraka.
Daga Kabiru Ado Muhd.