Labarai

An gano wanda yayi batanci ga manzon Allah a kasan hoton Rahama Sadau ba Kirista bane.

Spread the love

Da yammacin wannan rana ta Lahadi,wani mai suna Usman Sadau, ya wallafa a shafin sa na sada zumuntar Facebook cewa, “Jama’a ku kwantar da hankalin ku, mu dama mun san Rahama Sadau ba za tayi batanci ga annabi (S.A.W) ba, Kiristan da ake maganar yayi batanci ga annabi a kasan hoton Rahama Sadau bama Kirista bane”

Usman Sadau, wanda ake zargin ko Dan uwa me ga jaruma Rahama Sadau ya kara da cewa “Wallahi wani ne kawai da ba’asan ma addinin sa ba wasu makiyan Rahama Sadau a masana’antar Kannywood suka saka hada Baki da shi yayi wancan rubutun batanci domin a batawa Rahama suna.”

“Dama sun dade suna neman hanyar da za su sanya al’umma su tsaneta saboda sun ga tauraruwar ta tafi tasu basu samu ba sai yanzu, su kuma al’umma sun kasa fahimtar makiya ne ke bibiyar Rahama Sadau da sharri, anma kuma Allah yana nan kuma shine zai fitar da ita” Inji Usman Sadau.

Daga Shafin Hausa 7ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button