Labarai

An gano ‘yan matan da aka yi fataucinsu daga Osun a Kano ta hanyar gayyatar su Birthday – ‘yan sanda

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta cafke wani Adebisi Muideen da ya yi yunkurin safarar wasu ‘yan mata hudu daga Osun zuwa jihar Kano kan hanyar zuwa birnin Tripoli na kasar Libya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan SP Yemisi Opalola ta fitar.

“Wanda ake zargin ya gayyaci ‘yan matan zuwa bikin zagayowar ranar haihuwa a wani otel da ke Ile-Ife ya basu abinci da abin sha. Bayan sun ci abinci da abin sha ne ‘yan matan suka yi barci, daga baya kuma suka farka a jihar Kano kan hanyarsu ta zuwa Tripoli babban birnin kasar Libya,” inji ta.

Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa uku daga cikin ‘yan matan sun yi nasarar tserewa a Kano, inda daga bisani suka kira iyayensu, inda suka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

“Uku daga cikin ‘yan matan sun sake haduwa da iyalansu, amma har yanzu ba a san inda yarinyar ta hudu take ba,” in ji sanarwar ‘yan sandan.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ‘yan matan sun amince da su tafi Libya aiki.

Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa dan uwansa da ke zaune a birnin Tripoli ya umarce shi da ya samo masa wasu ‘yan mata sannan ya aika da su wurin wani mutum a Kano wanda zai kai su Libya.

“Wanda ake zargin ya ce a lokacin da ya isa gidan mutumin a Kano, ya hadu da ‘yan mata da dama da ake yi musu magani domin tafiya kasar Libya. ‘Yan sanda na binciken lamarin, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan kammala binciken mu,” in ji sanarwar.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button