Labarai

An Gargadi Buhari Kafin Ya Sauka Ya Tabbatar An Hako Fetur Din Arewa Da Kuma Kammala Aikin Jawo Ruwan Kogi zuwa Arewa, Sannan Kuma Ya Tabbatar An Daina Saida Kasar Najeriya Ga Kasashen Waje.

Spread the love


Tsohuwar kwamishinar lafiya a jihar Kano Hajia Amina, dattijuwa ce da taga jiya ta ga yau a Arewa ta ce “Kada shugaba Buhari ya kuskura ya gama mulkin shi bai yiwa arewa wadannan ababe guda uku ba, na farko kada yayi sake ya sauka ba a hako mai a Arewa ba, kada kuma ya sauka ba a jawo ruwa zuwa arewa aka soma sifiri don kawo kayayyaki ta cikin ruwa har arewa ba, haka kuma tace ayi hattara a daina saida kasar Najeriya ga kasashen waje.
.
Tayi wadan nan bayanan ne a cikin shirin Ra’ayi Riga na na BBC Hausa a ranar Juma’ar nan ta 2/10/2020.

Yankin Arewa dai yanki ne da aka haifi Shugaba Buhari, Wanda a yanzu haka shine yankin da yafi samun koma baya a kasar, domin yana fama da dumbin matsaloli kama daga bangaren ilimi, da rashin masana’antu, da koma bayan tattalin arziki, da rashin aikin yi, da kuma uwa uba rashin tsaron sa ya yiwa yankin zobe.

Daga Bappah Haruna Bajoga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button