An Hana mata musilmai daukar ciki a kasar Chana
Gwamnatin kwamunusanci na Kasar China ta hana mata Musulmi daukar ciki don rage yawan Musulmai da yaduwar Musulunci a fadin Kasar, mata Musulmai ‘yan kabilar Uighur na fuskantar cin zarafin hana su haihuwa a Xianjing na kasar China
China na daukar tsauraran matakan tilasta wa Musulmai ‘yan kabilar Uighur da wasu tsiraru rage haihuwa da zummar dakile yawan yaduwar al’ummar Musulmi, yayin da a gefe guda, gwamnatin kasar ke karfafa wa ‘yan kabilar Han-guiwar ci gaba da haihuwa.
A can baya, daidaikun mata Musulmai sun yi korafi game da tilasta musu takaita haihuwa, kuma wannan tilastawar ta dada tsananta a yanzu kamar yadda binciken kamfanin Dillancin Labaran AP ya nuna.
AP ya tattara alkalumansa ta hanyar amfani da kididdigar hukumomi da wasu bayanai na gwamnatin China da hirarrakin da ya yi da mutanen da aka tsare su a wani sansani saboda kin bin tsarin rage haihuwar.
Wasu masana sun bayyana wannan matakin na hana haihuwar da gwamnatin China ta fara aiwatarwa fiye da shekaru hudu a yankin Yammacin Xinjiang a matsayin wani nau’i na kisan kare dangi wa al’ummar Musulmi
Gwamnatin Xinjiang na tilasta wa matan da suka fito daga tsirarun kabilu Musulmai gudanar da gwajin juna-biyu akai-akai, kuma tana matsa wa dubban mata Musulmai zubar da ciki ko kuma ta cusa musu sinadaran hana daukar ciki a mahaifarsu, sannan Gwamnatin ta Xinjiang na garkame tare da azabtar da mutanen da suka ki bin tsarin takaita haihuwar kamar yadda binciken AP ya nuna
Jama’a wannan shine abinda yake faruwa a Kasar China, kuma idan wannan tsarin yaci gaba da gudana zasuyi wa Musulunci muguwar illa a Kasar, muna da gudunmawa na addu’ah da zamu bawa ‘yan uwa Musulmai na Kasar China, Insha Allahu majusawan China ba zasu taba cin nasaran kawar da Musulunci ba
Yaa Allah Ka daukaka Musulunci a Kasar China ta yadda makiya addininKa basuyi zato ba, Allah Ka tayar da Musulunci a Kasar China kamar yadda Ka tayar da Annabi Musa a gidan Fir’auna
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum