
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Mazauna Kauyen Gardawa dake Karamar Hukumar Funtu’a ta Jahar Katsina Sun Shaidawa Jaridar Katsina Daily Post Cewa An Kai Musu Hari.
Mazauna Kauyen Sunce A Jiya Talata da Misalin 12 na Dare ne Wasu yan Bindiga Suka Dira Kauyen Gardawa Sukayi Ta Harbe Harbe.
Sai dai Ba’a Samu Asarar Raiba sai dai Sun Gudu da Mutane 4 Mutu guda 1 Kuma Yanzu Haka yana Asbitin Funtu’a Yana Karbar Magani Saka makon Harbin Bindiga da Ya same shi.
Jahar Katsinar dai na Fama da Tashe Tashen Hankula Na Barayin Shanu da Masu Garkuwa da Mutane a Jahar ta Katsina.
Allah ya Shiga Tsakanin Nagari da Mugu!.