Labarai

An Jibge Jami’an Tsaro A Manyan Kasuwannin Kaduna.

Spread the love

Daga Muktar Onelove Kaduna..

A yau Laraba ne dai sassaucin dokar zaman gida da gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i yayi yafara Aiki.

A jawabin da gwamnan yayi jiya Talata, El-Rufa’i yace daga yau Laraba an sassauta dokar zaman gida, Inda aka bar Jama’a surika Zirga-zirga daga Litinin zuwa Juma’a tun daga kar 8 na safe zuwa 6 na yamman kowacce rana.

Gwamnan ya ce ranar Juma’a za a rika gudanar da sallar Juma’a, masu zuwa Chochi zasu Ringa zuwa duk Ranar Lahadi kadai, baya ga haka kuma ba a amincewa jama’a su ringa zuwa salloli biyar da aka saba ba, sannan kuma manyan Kasuwannin garin zasu cigaba da kasancewa a rufe, har sai bayan an sake yiwa dokar garambawul, Inji El-Rufa’i.

Sai dai kuma Jama’a da dama sunyi fitar farin dango Zuwa Kasuwanni da zummar suje su bude suci Gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu. To amma kuma sun tarar da Jami’an tsaro masu yawa a kofar Kasuwannin da kuma manyan hanyoyin da suka a kusa da Kasuwannin, wanda hakan yatilastawa jama’a komawa gidajensu.

Sai dai kuma masana da dama na hasashen cewa nan ba da dadewa ba suma Kasuwannin za a budesu, duba da yawancin garuruwan da suke makwabtaka da Kadunan duk sun bude Kasuwanninsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button